DuniyaLabarai

Sakataren APC na Gombe ya soki Isa Ali Pantami a Fili

​A wani taro da aka gudanar kwanan nan, Sakataren Tsare-tsare na jam’iyyar APC na jihar Gombe, Saleh Dan’iya, ya fito fili ya bayyana bacin ransa ga Isa Ali Pantami.

Sakataren ya zargi Pantami da rashin taimaka wa ’ya’yan jam’iyyar APC na jihar Gombe a lokacin da yake rike da babban mukami na Minista.

Ya bayyana cewa duk wadanda ke cewa suna goyon bayan Pantami a wurin taron, “karya suke yi”, kuma a zahiri kowa bacin rai yake ji da shi.

Dan’iya ya jaddada cewa ya dace a gaya wa Pantami gaskiya domin bai yi amfani da damar da ya samu wajen inganta rayuwar mabiyansa ba.

Shin kuna ganin Sakataren APC ya yi daidai da ya fadi wannan maganar a gaban Pantami?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button