DuniyaLabarai

Wani Sabon Ango Ya Shigar Da Karar Amaryarsa Kotu Bayan Gano Tana Da Juna Biyu Na Wata Uku

Wani sabon biki da aka gudanar kwanan nan ya koma kura-kurai da rudani, bayan da ango, Malam Dahiru Yakubu, ya garzaya kotu domin neman a raba aurensa da amaryarsa sannan a mayar masa da kudaden da ya kashe.

Rahotanni sun bayyana cewa mako guda kacal bayan tarewar amarya a gidan mijinta, ta fara nuna alamun rashin lafiya mai tsanani. Da farko, angon ya zata rashin lafiyar canjin yanayi ne, sai dai bayan an garzaya asibiti domin yin gwaje-gwaje, sakamakon ya nuna cewa amaryar tana da juna biyu na tsawon wata uku (3).​Wannan lamari ya girgiza ango da sauran dangi, ganin cewa auren nasu bai kai mako biyu ba da

Ganin hakan, Malam Dahiru bai yi wata-wata ba ya shigar da kara gaban kotu. Babban burinsa shi ne: ​A soke auren tunda an yaudare shi.​ A mayar masa da kudin sadaki da sauran kudaden da ya kashe wajen hidimar biki.​ A biya shi asarar da ya yi na kayan lefe da sauran kayayyaki.

​A daya bangaren kuma, dangin amaryar sun bayyana nasu korafin, inda suma suka shigar da kara suna neman kotu ta basu damar kwashe kayan dakin amaryar da take ciki.

Wannan labari ya karade gari inda mutane da dama suke bayyana ra’ayoyinsu. Wasu na ganin ya kamata iyaye su rinka bincike da sanya ido akan tarbiyyar ‘ya’yansu kafin lokacin aure, yayin da wasu kuma ke ganin wannan wani babban kalubale ne ga tsarin aurenmu na yau.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button