DuniyaLabarai

Jita-jitar Mutuwar Ali Khamenei: Gaskiya ko Karya?

A kwanan nan, tsohon shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya fito ya bayyana cewa shugaban kasar Iran, Ali Khamenei, ya riga ya mutu. Trump ya yi wannan ikirari ne a shafinsa na Truth Social, inda ya kwatanta Khamenei a matsayin daya daga cikin “mugayen mutane” a tarihi, sannan ya kara da cewa harin da Amurka ta kai ya yi sanadiyyar rugujewar mafakar shugaban.

Duk da wannan ikirari na Donald Trump, gwamnatin kasar Iran da kafafen yada labaranta sun fito sun karyata wannan labari. Sun bayyana cewa shugaba Khamenei yana nan da ransa kuma yana cikin koshin lafiya. Har ma an fitar da wasu bidiyoyi da ake ikirarin na kwanan nan ne domin tabbatar wa duniya cewa bai mutu ba.

Trump ya ce Khamenei ya kasa tsira daga fasahar leken asiri ta Amurka wadda ta bibiyi inda yake.

Trump ya yi kira ga sojojin Iran da su daina goyon bayan gwamnatin kasar su koma bangaren jama’a domin kafa sabuwar gwamnati mai adalci.

Har yanzu babu wani babban kafar yada labarai na duniya da ya tabbatar da mutuwar Khamenei, kuma bidiyoyin da Iran ke fitarwa suna nuna akasin abin da Trump ya fada.

Masana na ganin cewa wannan wani bangare ne na yakin cacar baka tsakanin Amurka da Iran, kuma ya kamata a bi diddigin labarin kafin yanke hukunci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button