
cewar ubangiji Usman Ibrahim wato Evangelist Ibrahim Dikko yace Daga jiya zuwa yau, ya samu sakonni da kiran waya masu yawa a kan Usman Ibrahim, wanda labari ya bazu cewa ya koma addinin Musulunci. Mutane da dama suna kiransa ne domin jin ta bakinsa, da tunanin cewa shi ne uba a gare shi ta fannin ruhaniya.
Evangelist Ibrahim Dikko yace Ina so ’yan’uwa su sani cewa, Usman Ibrahim ba almajirina ba ne, kuma bai taba kasancewa karkashin kulawata ba. Na san shi ne a makarantar horar da masu bishara (disciple school) ta Abubakar Maigudma. Usman bafullatani ne da ya karbi Kiristanci shekaru uku da suka wuce, kuma a watan jiya ne aka yi masa baftisma.
Ta yaya mutumin da ko baftisma bai yi ba zai kira kansa “Evangelist” (Mai Bishara)? Wane ne ya nada shi? Duk wadannan abubuwa da yake wallafawa a Facebook da sunan Evangelist, karya ne kawai da neman suna
Usman ya yi ikirarin kasancewa karkashin marigayi Rev. Azzaman. Gaskiya ne cewa Rev. Azzaman ya gabatar da shi a kafofin sada zumunta, amma abin takaicin shi ne, kafofin sada zumunta sun bata Usman. Wannan babban kuskure ne da muke yi na tallata almajiran da ba su nuna gaskiya da tuban kirki ba.
A lokacin jana’izar Rev. Azzaman, Usman ya kira ni yana neman taimakon kudin mota domin shi da abokinsa Yar Zuru su zo Kaduna, kuma na taimaka musu. Bayan jana’izar, na zaunar da shi na ba shi shawarwari kamar haka:Na ce ya koma makaranta ya ci gaba da karatu.Na gaya masa ya daina yaudarar kansa da sunan “Evangelist” a Facebook.Na umarce shi da ya daina hulda da mata, shan taba, da shan giya, domin an kai min korafin cewa har yanzu yana yin wadannan abubuwan.Na gaya masa ya nemi sanin Kristi da gaske, domin ba zai yiwu ya yi aikin Allah da tsohuwar dabi’a ba.
Fiye da watanni bakwai da suka gabata, na goge lambarsa kuma na daina biye masa a Facebook. Duk lokacin da ka ba shi shawara, sai ya koma Facebook ya fara zaginka ko cin mutuncinka. Ya yi wa Rev. Mohammed haka, kuma ya yi min ni kaina. Domin gudun kada ya ja ni a fagen tatar da juna a fili, na yanke shawarar yin watsi da shi tare da cire shi daga rukunin tafiyar Azzaman.