DuniyaLabarai

Bikin “Ranar Fy*de ta Duniya” a Delta: Gaskiya ko Almubazzaranci?

A kwanakin nan, wasu bidiyoyi sun karade kafafan sada zumunta musamman a Najeriya, inda aka ga wasu matasa a garin Ozoro dake jihar Delta suna gudanar da wani biki da suka kira da “World Rpe Day” (Ranar Fyde ta Duniya).

​A cewar rahotanni da bidiyoyin da ke yawo:​Matasa maza ne ke fitowa kan tituna suna tursasa mata.​Suna cin zarafin mata ta hanyar taba jikinsu ko yaga musu tufafi.​An bayar da gargadi ga mata da kada su kuskura su fito waje a lokacin da ake gudanar da wannan al’ada wacce aka ce tana daukar tsawon kwanaki bakwai.

Wannan lamari ya janyo bacin rai daga bangarori daban-daban.

Mutane da dama sun bayyana wannan biki a matsayin “jahilci” da kuma babban kalubale ga hakkin dan Adam da mutuncin mata.

Kamar yadda Alhaji Abisunuhu ya bayyana a bidiyonsa, akwai korafin cewa idan irin wannan danyen aikin ya faru a wasu sassa na Najeriya (musamman Arewa), kowa tashi yake ya dinga suka, amma ga shi wannan ya faru amma wasu na kokarin nuna kamar al’ada ce kawai.

Akwai kira mai karfi ga jami’an tsaro da gwamnatin jihar Delta da su sa baki domin dakatar da wannan al’ada da ke barazana ga tsaron mata.

Duk da cewa wasu na kokarin fakewa da sunan al’ada, dokokin Najeriya da ma addinan duniya sun haramta cin zarafin mace ko taba jikinta ba tare da izininta ba. Wannan biki ba wai kawai ya sabawa tarbiya ba ne, har ma laifi ne babba a karkashin dokar kasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button