
Babban attajirin nan na Afirka, Alhaji Aliko DBabban attajirin nan na Afirka, Alhaji Aliko Dangote, ya fitar da wani gagarumin gargadi ga al’ummar Najeriya game da takun-sakar da ake yi tsakanin kasashen Iran da Isra’ila.
A cewar Dangote, muddin wannan rikici ya kazance har aka kai ga rufe hanyar ruwa ta Strait of Hormuz, to fa tattalin arzikin duniya zai girgiza, wanda hakan zai taba Najeriya kai-tsaye. Ya bayyana cewa wannan matsalar na iya jefa kasar nan cikin wani hali na matsin tattalin arziki mai kama da wanda aka fuskanta a lokacin kulle (lockdown) na cutar COVID-19.
Strait of Hormuz ita ce babbar hanyar da man fetur din duniya ke bi. Rufe ta zai janyo tashin farashin kaya da wahalar kayayyakin bukatu.
Dangote ya nuna cewa Najeriya na bukatar yin shiri sosai don gudun fadawa cikin mawuyacin hali idan aka samu tsaiko a harkar sufurin jiragen ruwa na kasa da kasa.
Wannan magana ta Dangote ta tayar da hankulan masana tattalin arziki da dama, inda suke ganin cewa ya kamata gwamnatin tarayya ta fara daukar matakan kariya tun kafin abubuwa su jagule.