A kwanakin nan ne hotuna da bidiyon wata makarantar firamare da babban mai kera bidiyoyin fadakarwa da bincike a shafukan sada zumunta, Dr. Bello Galadanchi (wanda aka fi sani da Dan Bello), ya gyara ta dauki hankalin al’umma tare da haddasa ce-ce-kuce mai zafi.
Shahararren dan jaridar ya fitar da kudadensa na kashin kansa masu yawa domin sauya wa makarantar zubi, inda aka fente ginin da launuka masu kayatarwa daban-daban da nufin samar da yanayi mai kyau na koyo da koyarwa ga yaran talakawa. Sai dai kuma, wannan fasali na launukan fentin ya janyo surutai a tsakanin wasu al’umar Arewa a shafukan sada zumunta, inda wasu ke zargin cewa launukan sun yi kama da tutar “Rainbow” da ke inganta madigo da luwadi (LGBTQ+).
A martanin da wani matashi ya mayar ta hanyar bidiyo, ya fito fili ya kare Dan Bello daga wadannan zargi. Matashin ya nuna bacin ransa kan yadda mutane ke saurin gurgunta gwiwar masu alheri, inda ya bayyana cewa kuskure ne babba a rika suka ko zargin mutumin da ya sadaukar da dukiyarsa wajen tallafa wa ilimin yara, musamman a daidai lokacin da hukumomi da gwamnati suka kasa tabuka abin a-zo-a-gani a harkar ilimi.
Matashin ya bayyana cewa: “Muna bukatar mutane irin su Dan Bello da yawa a Arewa wadanda za su rika gyara mana makarantunmu da suka lalace. Idan sun gyara, ko ma wace irin dabba ko fenti za su sanya a jiki, mu ba ruwanmu, mu dai a gyara mana makarantunmu domin yaranmu su sami damar yin karatu cikin sanyi da kwanciyar hankali.”
Daga karshe, ya yi kira ga al’umma da su daina shafa wa masu kishin kasa kashin kaji, sannan ya yi wa Dr. Bello addu’ar fatan alheri tare da fatan samun wasu masu kudin da za su yi koyi da wannan kyakkyawan aiki domin ciyar da yankin Arewa gaba.