Wani mummunan hatsarin mota ya faru a garin Damagum da ke karamar hukumar Fune a jihar Yobe, inda wata motar fasinja ta bi ta kan wasu mutane da ke tsaka da gudanar da sallar juma’a a kan titi.
Rahotanni sun nuna cewa motar, kirar Hummer Bus (18-seater), tana kan hanyarta ne daga Damaturu zuwa Bauchi lokacin da direban ya rasa iko da motar, wanda ya yi sanadiyar afkawa cikin masallatan.
Mutane da dama sun rasa rayukansu nan take.
Fiye da mutane 27 sun sami munanan raunuka, inda aka garzaya da su asibitin koyarwa na jami’ar jihar (Yobe State University Teaching Hospital) da ke Damaturu domin karbar magani cikin gaggawa.
Bayan faruwar lamarin, matasan garin Damagum sun fito cikin fushi inda suka tare motar tare da banka mata wuta. Wannan lamari ya janyo tsaikon ababen hawa a babbar hanyar da ta hada Kano da Maiduguri na tsawon lokaci.
Wannan hatsari ya sake rura wutar muhawara a shafukan sada zumunta da ma cikin al’umma game da:
Shin ya dace a rinka toshe manyan hanyoyi domin gudanar da salla?
Yaya ya kamata hukumomi su takaita gudun ababen hawa a cikin garuruwa don kaucewa irin wannan asarar?
Hukumomin tsaro da na kiyaye hadurra (FRSC) sun bukaci direbobi da su rinka kiyaye gudun tsiya, sannan sun shawarci al’umma da su kiyaye gudanar da ibada a wuraren da za su iya jefa rayuwarsu cikin hadari.