A wani mataki da ya girgiza fagen siyasar Najeriya, tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party, wanda kuma ya taba kasancewa a jam’iyyar ADC (African Democratic Congress), Mista Peter Obi, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar.
Kodayake tsohon gwamnan na jihar Anambra bai fito fili ya bayyana takamaiman inda ya dosa ba, majiyoyi na kusa da shi sun nuna cewa wannan mataki ya biyo bayan Rashin jituwa kan tsare-tsare: Akwai rahotannin dake nuna rashin daidaito tsakanin salon siyasarsa da kuma shugabancin jam’iyyar.
Peter Obi ya jima yana kira ga hadin kan dakarun adawa domin fuskantar kalubalen dake gaban kasa, kuma ficewar tasa na iya zama wani bangare na shirin kulla wata sabuwar tafiya.
Wasu na ganin rikicin cikin gida da ya addabi jam’iyyar ADC a matakin kasa ya taimaka wajen yanke wannan shawara.
”Siyasar Peter Obi tana karkata ne ga abin da talaka yake so, kuma idan ya ga tafiya ba zata kai ga nasara ba, ba ya jinkirin neman mafita,” in ji daya daga cikin masu sharhi kan al’amuran yau da kullum.
Har yanzu magoya bayansa, wadanda aka fi sani da ‘Obidients’, suna jiran jin mataki na gaba. Shin zai koma tsohuwar jam’iyyar sa ta Labour Party, ko kuwa akwai wata sabuwar hadaka (Merger) da ake shiryawa da sauran manyan yan siyasa?